Misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news
A ƙaramar hukumar Batsari dake jihar Katsina, al’umma na kokawa gameda shirin babban bankin ƙasar na sauya fasalin takardun naira.
Bincike ya nuna cewa akwai tsofaffin takardun ƙuɗin a hannun mutane kuma suna ƙoƙarin ɓatar da su amma abun yana neman gagarar kwandila, ta yadda abun ya zama gaba kura baya sayaki, domin ƴan kasuwa na yankin sun fara ƙin karɓar kuɗin, wasu da dama sun kulle shagunan su saboda kada a kawo masu tsofaffin kuɗin. Wannan dalilin yasa sarkin Ruma Katsina hakimin Batsari Alhaji Tukur Muazu Rumah yasa akayi shela a ranar asabar 21-01-2023 cewa duk ɗan kasuwar da yaƙi karɓar kuɗin zai fuskanci hushin hukuma tunda lokacin rufe karɓar kuɗin bai yi ba. Amma duk da haka mutane na fama da turjiyar ƴan kasuwa.
Wata matsalar da lamarin ya haifar shine, yadda ake shan wahaka kafin a shigar da su a asusun ajiyar bankuna, saboda wasu sun bayyana mana cewa sun shafe kwana da kwanuka suna zarya a banki amma basu samu halin shigar da kuɗin ba.
Sannan abun ya haifar da ƙaranci da tsadar kayayyakin abinci, inda takai ga ana saida kwanon masara (tiya ɗaya) naira ɗari bakwai, babbar matsalar ma bata samuwa a wajen masu saidawa sai ɗaiɗaiku.