…yayin da Sheikh Bala Lau ya ziyarci Shugaban NDLEA
Shugaban kungiyar Izala na tarayyar Nijeriya, Ash-sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa kungiyar IZALA ta kebance daya daga cikin manyan makarantun ta a jihar Kaduna, don inganta shi zuwa gidan jinya ga masu Shaye-Shaye na zamani wanda za’a karbi masu fama da lalalurar Shaye-Shaye a sauya musu tunani kuma su fito da haddan Al-Qur’ani Maigirma.
Sheikh Bala Lau ya bayyana hakan ne a wani bayani da ya rattabawa hannu ga manema labaru kuma ya saka a shafin sa, inda yace a ranar Laraba ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ofishin shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) Janar Buba Marwa mai ritaya.
Bala Lau ya bayyana cewa shugaban hukumar NDLEA ya jinjinawa kungiyar IZALA bisa wannan kokari, kuma ya nemi sauran kungiyoyi da su kwaikwayi wannan yunkuri, a matsayin gudunmawa ga yaki da miyagun kwayoyi wanda ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma.
Ita ma hukumar NDLEA ta fitar da bayanai, ta hannun mai magana da yawun bakin hukumar Femi Babafemi, inda hukumar tace ziyarar shugaban ya kara jaddada bukatuwar hadin kai tsakanin shugabannin addinai da kuma hukumomin gwamnati, don cigaban al’umma.
Idan ba a manta ba dai, yanzu haka IZALA tana gina jami’a a jihar Jigawa, wanda ta kaddamar a shekarar 2020 kuma ta sanyawa suna As-Salam University.