Iyayen sauran ɗalibai 11 da a ka yi garkuwa da su a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke garin Yauri a Jihar Kebbi, sun fara shiri na tara kudin fansa Naira miliyan 100 domin a sako ƴaƴansu.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a ranar 17 ga watan Yuni, 2021, aka sace dalibai sama da 80 a lokacin da wasu ‘yan bindiga, karkashin jagorancin wani ƙasurgumin ɗan fashin jeji, Dogo Gide suka kai hari makarantar.
Daga baya an sako yawancin daliban ga gwamnatin jihar bayan an biya kudin fansa.
Sai dai bayan watanni 19 ‘yan ta’addan na ci gaba da tsare 11 daga cikin daliban, inda suke neman kudin fansa Naira miliyan 100.
Da suke magana da jaridar Daily Trust a ranar Lahadi, iyayen daliban da aka sace da suka hadu a harabar makarantar sun koka kan yadda suka yanke shawarar daukar al’amura a hannunsu bayan gwamnati ta gaza musu.
Shugaban kungiyar iyayen, Salim Kaoje, ya bayyana cewa sun tattauna da Gide tare da taimakon mahaifiyar sa, wadda ya ce tana kara matsa masa lamba kan ya sako ƴan matan.
“Mun tattauna da Dogo Gide ne a ranar 15 ga watan Disamba 2022, da farko ya ki amincewa da duk wani yunkurin tattaunawa da mu, amma bayan da mahaifiyarsa ta shiga tsakani, ya amince ya sako yaran mu idan muka biya kudin fansa naira miliyan 100, in ba haka ba, ba za mu sake ganin ƴaƴan mu ba.
“Ya bayyana karara cewa idan har ba mu hada kuɗin da ya nema ba, ba za mu sake gani ko jin ɗuriyar ‘ya’yanmu ba, kuma wannan ne ya sa muka taru a matsayin iyaye domin yin wannan roko,” inji shi.
Kaoje ya ce kowanne daga cikin iyayen ya kuduri aniyar sayar da duk wani abu da ya mallaka da suka hada da kadarorin kasa da sauran kayayyaki masu daraja, domin samun damar tara kuɗin don a sako ƴaƴan na su.