Duk kuma wanda ya cike aikin ya fitar da slip, to sunansa ya fita ya shirya zuwa tantancewar
Daga, Ibrahim M Bawa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta fara tantance waɗanda suka cike neman aikin zabe mai zuwa, wato PO da kuma APO
Kamar yadda Katsina Daily News ta sami karin bayani daga hukumar zabe reshen jihar Katsina, an fara tantance waɗanda suka nemi aikin ne daga yau Laraba, har zuwa ranar 23 ga wannan watan na Janairun 2023, a ofishin zabe na kananan hukumomin jihar Katsina 34.
Haka kuma, duk wanda ya san ya cike neman aikin, kuma an turo masa sakon slip mai dauke da hotonsa ta email dinsa, ko an kafe sunansa ko ba a kafe ba, sunansa ya fita, ya garzaya ofishin zabe na karamar hukumarsa don tantance shi.
A tantancewar, ana bukatar duk wanda ya cike aikin, ya je da takardun da ya bayyana cewa yana dasu, a lokacin da ya cike neman aikin ta manhajar INEC dake intanet.
Daɗin dadawa, waɗanda suka nemi aikin masu duba ma’aikatantan zaben wato supervisors, za a sanar da ranar da za a tantance su a shalkwatar zabe dake Katsina.