Hazikin matashin dan siyasar jihar Katsina kuma Darakta Matasa a kwamitin yaƙin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar da Sanata Yakubu Lado Danmarke ya bayyana cewa yana da tabbacin al’ummar jihar Katsina, sun shirya tsaf domin dawo da jam’iyyar PDP a jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Honarabul Musa Yusuf Gafai wanda shi ne Darakta Janar na shahararriyar kungiyar nan ta Ladon Alkhairi ya bayyana haka a wata sanarwa manema labarai da ya fitar a jiya Alhamis.
Shugaban matasa a kwamitin yaƙin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da kuma dan takarar gwamnan jihar Katsina, Alhaji Yakubu Lado Danmarke, Honarabul Musa Yusuf Gafai ya kara da cewa ina godiya ga al’ummar jihar Katsina musamman matasa da mata na irin goyan bayan da yan takarar jam’iyyar PDP ke samu a yaƙin neman zaben da muke shiga lungu da sakon jihar Katsina, da ke gudana a halin yanzu, wannan ya nuna al’ummar jihar Katsina sun shirya tsaf, domin dawo da mulkin adalci na jam’iyyar PDP a jihar Katsina da Najeriya ba ki ɗaya.
Honarabul Musa Gafai kuma Darakta Janar na Ƙungiyar Ladon Alkhairi a jihar Katsina ya ci gaba da cewa ina kara jawo hankalin iyayen mu mata da su guji masu yaudarar su suna karɓar masu katin zabe da sunan za su ba su tallafi, su yi karatun ta natsu ranar zaɓe, da su zaɓi nagartattun yan takarar da jam’iyyar PDP ta tsaida a kowane matakai domin samun sauƙin rayuwa.