Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News
Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula (Coalition Katsina Groups) karkashin Jagorancin Comrade Hamza Umar Saulawa, sun shirya gagarumin taron nuna goyon baya ga Dantakarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC Malam Bola Ahamed Tinubu.
Taron ya ya samu halartar Manya kuma Jajirtaccin ‘Yan Siyasa a jihar Katsina, da Malamai na Addini, Matasa Maza, da Mata.

Da yake jawabi a wajen taron Shugaban gamayyar Kungiyoyin na Fararen Hula, Comrade Hamza Umar Saulawa ya bayyana kokari, kishi da son cigaban Arewacin Najeriya da Dantakarar yake dashi, yace ba zaka taba gane haka ba sai ka rabeshi.
Saulawa ya bayyana cewa, “Bola Ahamed Tinubu ya kawoma jiharsa ta Legas gagarumin cigaba, ta fannonin, tsaro, Kasuwanci, gine-gine da samar da Aikin yi.” Yace Bola shine Bayerabe na farko da ya janyo Kabilun Najeriya daban-daban ciki hadda Hausawa, ya basu Mukaman Gwamnatin jiharsa ta Legas domin hadinkan kasa da daidaito.
Hamza ya kara bayyana yanda Bola Tinubu ya jajirce da Kudinsa Iya Siyasarsa ya dafama Shugaba Muhammad Buhari har ya zama Shugaban Kasa, bayan da ya fito Takara sau hudu bai samu Mulki ba yace don haka kin zabar Bola Tinubu ga Dan Arewa kamar cin Amana ne, don haka yanada kyau mu fitar da kabilanci daga Zuciayarmu mu zabi Bola Tinubu” injishi.
Da yake tsokaci a wajen taron Matashin Dansiyasa Hon. Muntari JBO ya bayyana bambance-bambance dake tsakanin Atiku Abubakar da Bola Ahamed Tinubu, inda ya kawo musalai na cigaba wanda Atiku ya gaza samar dasu duk da ya zamo na biyu mafi karfin iko a Najeriya.
Taron da aka gudanar a babban wajen taro na Katsina Motel ya hado Kungiyoyi mabanbanta daga ko ina a jihar Katsina, ‘Yansiya da sauransu.