Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jerin sunayen’Yan takarar shugaban kasa na shekarar 2023, jerin sunayen na farko. Bayanin hakan ya fito daga wata sanarwa daga hukumar a Abuja. Bayanan da jerin sunayen suka kumsa harda Asalin yanki da shekaru da Matakin karatu da sauran bayanan wadanda zasuyiwa ‘yantakar mataimaka.
Yantakar da sunayensu suka bayyana akwai na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar Da Bola Ahamed Tinubu na jam’iyyar APC da Pita Obi na jam’iyyar Labour Party da Dakta Rabi’u Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP.
A sanarwar da shugaban kwamitin Ilmantar da masu kada kuri’a Festus Okoye ya fitar, ya kuma bayyana bayanan da suka safi ‘yan takarar, sanarwar ta bayyana cewa akwai masu bukata ta musamman akalla gima sha daya da suka fito takara ta mukamai daban-daban