Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta bayyana fara raba katin Zabe a ranar Litinin 12 ga watan Disamba, a dukkanin faɗin Najeriya.
Kamar yanda sanarwar ta riski Katsina City News ta bakin PRO na shiyyar Katsina ya bayyana cewa: za’afara bada Katikan ne a Ofisoshin Hukumar na Ƙananan Hukumomi.
A Katsina ma za’a fara raba katin a ofishin INEC na Ƙaramar hukumar Katsina, kuma sanarwa ta ce, rabon katin zaici gaba har ranakun Asabar da Lahadi.
Zasu duba yiyuwar faɗaɗa bada katin ga Mazaɓu daga 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan.
Source:
Katsina City News
Via:
Katsina City News