Hukumar NDLEA ta gano tafkekiyar gonar wiwi a Katsina
Hukumar dake hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa watau NDLEA ta gano wata ƙatuwar gonar dake shuka tabar wiwi a ƙaramar hukumar Dutsi ta jihar Katsina.
Mataimakin shugaban rundunar hukumar na jihar Katsina dake kula da aiki da bayar da horo, Hamidu Halidu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin hukumar.
A cewar sa, tuni jami’an hukumar suka kama wani mai suna Mas’udu Bukar wanda ake zargi da mallakar gonar kuma yanzu haka suna kan
bincike da zarar sun kammala za su kai shi kotu.
Halidu Hamidu ya cigaba da cewa wannan ne karo na farko da hukumar ta taɓa gano inda ake shuka wiwi a jihar kuma hakan ba ƙaramar barazana ce ba ga al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Haka zalika jami’an hukumar sun bayyana samun nasarar kama kwalebanin maganin mura samfurin kodin har kwalba 1740 da kuma fakitin kwayar Tramadol 80 duk dai a jihar ta Katsina.
A cewar sa, kayan laifin da hukumar ta kama cikin ɗan lokacin nan sun kai na darajar Naira miliyan 15.