Hukumar Ilimin Kimiyya da Fasaha a ƙarƙashin ma’aikatar Ilimi ta jihar Katsina wato (Science and Technical Education Board) a Turance, ta shirya Rangadi ga makarantun Sakandare na jihar Katsina.
Domin gani da ido Irin yanda Makarantun ke gudanar da Koyarwa, gami da sa ido da bada Shawarwari.
Ziyarar gani da idon wadda Hajiya Laraba Lawal Usman, Maƙaddashiyar Sakatare a ma’aikatar, tare da Daraktoci da sauran ma’aikatan hukumar Ilimi ta kimiyya da fasaha ta jihar Katsina, sun fara daga Sakandaren ‘Yan mata ta garin Ƙanƙara a ranar 8 ga watan Nuwamba, inda suka ƙarƙare Ziyarar a Makarantar Sakandaren garin Ɓatagarawa a ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba.
Hajiya Laraba Lawal Usman da ‘Yan tawagarta sun yaba da ganin yanda makarantun suke gudanar da Ayyukan su, da bada Shawarwari domin haɓaka Ilimin ɗaliban na jihar Katsina.
Makarantun sun haɗa da; Makarantar Mata ta kimiyya da fasaha a garin Charanci, Makarantar Mata ta kimiyya da fasaha a garin Ajiwa, Makarantar Kwana ta Maza dake garin Mashi, Makarantar Sakandaren Kimiyya da fasaha ta garin Funtua, Makarantar Sakandaren Kimiyya dake garin Malumfashi, sai makaranta kimiyya da fasaha ta garin Sandamu.
Da sauran Makarantun na Kimiyya da Fasaha dake faɗin jihar Katsina ga baki ɗaya