SANARWA
Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa National Population Commission NPC ta ɗage ranar da zata bada Horo ga ma’aikatan wucin gadi
Hukumar na son sanar da jama’a cewa an dage horas da masu duba da kididdigar matakin karamar hukumar da aka shirya za a fara gobe 13 ga Afrilu, 2023 saboda wasu dalilai, sana ta bayyana cewa zata sanar da wata ranar a nan gaba.
Ta bayyana cewa “Muna sanar da ‘Yan Najeriya cewa, Hukumar ta jajirce wajen ganin tayi sahihin Aikin Ƙididdiga mai Inganci domin tantance yawan jama’a, kuma shirye-shiryen sunyi nisa.”
Hukumar kuma tayi kira ga al’umma da suyi watsi da duk wani sako da ya saɓawa wannan, sana kuma hukumar tana bada hakuri game da wannan sauyin lokaci da aka samu.
