Hoton Babba Ɗan Yakubu Lado Saman Mota Wurin Kamfen Ya Ja Hankalin Mutane A Katsina
Wani hoto dake dauke da babban ɗan ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Danmarke, Sadiq Lado a saman mota wurin gangamin yaƙin neman zabe ya ja hankalin al’umma da dama a jihar Katsina.
Wannan dai watakila ya faru ne sakamakon rashin sabawa da aka yi da ganin hakan a tsakanin yan siyasa a
A lokutta da dama dai ana zargin ƴan siyasar da ɓoye ƴaƴan su na cikin su a gida ko ma a kasashen waje lokacin da suke yaƙin neman zaɓen su amma su riƙa tafiya da ƴaƴan wasu.
Sai dai a iya cewa a wannan karon, lamarin ya bambanta a jihar Katsina inda aka ga babban ɗan ɗan takarar a saman wata mota mai dauke da sifiku a wurin gangamin yakin neman zaben mahaifin sa a daya daga cikin kananan hukumomin jihar Katsina.