
Hazikin matashi kuma daya daga cikin jagoran matasan jihar Katsina, Honarabul Musa Yusuf Gafai ya zama kwamandan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da dan takarar gwamnan jihar, Sanata Yakubu Lado Danmarke a bangaren matasa a jihar Katsina.
Bayanin haka na cikin wata takarda nadinsa da Darakta Janar na yaƙin neman zaben, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa ya sanya wa hannu.

A cikin takardar an bayyana cewa an yi nadin bisa ga cancanta da kuma kwazon da ka nuna a tafiyar PDP a jihar Katsina, wannan dalilin ya sa kwamitin yakin neman shugaban kasa ya amince da nadin na jagorantar matasa a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa da dan takarar gwamnan jihar Katsina, Alhaji Yakubu Lado Danmarke.
Daga karshe kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ya taya matashin Honarabul Musa Yusuf Gafai bisa ga wannan muƙamin tare tabbacin yana da rawar da zai taka don ganin yan takarar dake karkashin jam’iyyar PDP sun samu nasara a matakai daban-daban.