Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Majalisar samar da tsaro a Najeriya ta bayyana kokarin da take na ganin ta samu ceto sauran Fasinjojin jirgin kasa da masu garkuwa da mutane suka rike a watannin baya.
Ministan ma’aikatar ‘Yansanda, Mai gari Dingyadi ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala zaman majalisar a fadar shugaban kasa.
Taron na majalisar shugaban kasa wanda shuba Buhari ya jagoranta, duka manyan rundunoni tsaron kasa sun samu halartar, bayan kammala taron, ministan harkokin cikin gida Ra’uf Aregbesola ya sanar da cewa shugaban kasa yayi farinci matuka a yanda ake samun nasarar samar da tsaro a kasar, musamman ayyukan da sojoji da ‘yan sanda suke yi. A nasa bayanin Ministan ‘Yansanda Maigari Dingyadi yace kame wanda ke shiga tsakanin wadanda akai garkuwa dasu da iyalansu ba zai sa gwamnati tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa ta ceto sauran wadanda ke hannun masu garkuwar.
A cewar Dingyadi shine kawai wanda ya nuna kansa a matsayin mai shiga tsakani ‘yan ta’addan da iyalansu, amma akwai mutane da dama wa’danda gwamnati tasan da zamansu kuma suke yin wannan aikin.
Mai gari ya yabawa jami’an tsaron kasar saboda jajirce da namijin kokari da suka rika nunawa a wajen tabbatar da ganin cewa sun yaki ‘yan ta’adda dakuma kawar da masu sace mutanen. Yace Gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar nan da ake cewa (National Tasks Force) da suka ce suna yaki da masu shigowa da makamai da kuma fasa Bututu, yace an haramta su ne domin gwamnati bata amince da Kungiyar ba. Yace “mu a iya saninmu dai ‘Yansanda na Gwamnatin tarayya ne, amma al’umma idan suna son ‘Yansandan jihohi sunsan hanyar da suke bi su samesu, suna gabatar da maganganu ga wakilan su, kuma wakilan su dauka, sukai majalisa idan abin ya fito a Dokance Gwamnatin tarayya bata da wani abinda zatayi illa ta kaddamar da shi.”
Mai gari Dingyadi ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike akan fasa gidan gyaran hali na Kuje dake Abuja inda ya tabbatar da cewa Gwamnati zatayi duk mai yiyuwa wajen gano hakikanin masu hannu a hakan kuma a hukunta duk wanda wanda ake tabbar da hannun nasa, Ministan ya kara Jinjinawa ‘yansanda akan zaben da aka gudanar da jihohin Osun, Ekiti da Anambra.