Zaharaddeen Ishaq Abubakar
An shiga Sati na hudu da harin garin Bakiyawa dake karamar hukumar Batagarawa a cikin jihar Katsina, inda a watan Satumba da ya gabata mahara suka shiga garin sukayi kan mai uwa da wabi, inda suka tafi da Kusan mutum Hamsin tsakanin Maza da Mata.
Aminu Mannir Bakiyawa na daya daga cikin wadanda aka sace matar sa domin neman kudin fansa, ya shedawa Jaridar Katsina City News cewa “Yau kwana Ashirin da hudu da sace mana dangi da matayen mu, amma duk da muna cikin Lokacin Siyasa, babu wani mai neman Kujera ko wadanda ke ci, da ya iya zuwa ya jajanta mana akan abinda ya faru damu.” Aminu ya yaba ma Shugaban karamar hukumar Batagarawa inda yace shi kadai ne yazo yayi masu Jaje.
Majiyar ta Katsina City News ta tabbatar da Sace Mata Ashirin da hudu da Maza Ashirin ko da yake daga bisani sun saki mace daya daya, ba tare da biyan wata diyya ba kuma sun aiko ta da takardar bukatarsu. Wanda ya nuna cewa a halin yanzu akwai Mutane Arba’in da uku a wajensu, Maza ashirin mata ashirin da Ukku, inda suka nemi abasu Naira miliyan dari biyu da hamsin.
Majiyar Katsina City News ta jiyo cewa mutanen Bakiyawa sun nemi a basu ‘yan uwansu akan Naira miliyan goma inda su barayin suka kare su da zagi da cin mutuncin sakamakon tayin da sukayi.
Da muke tuntubar wadanda abin ya shafa game da halin da iyalan nasu suke ciki, sai suka shedamana a cewa a ranar Talata da ta gabata barayin sun kira mafiya yawa daga cikin ‘yan uwan, Iyalan da suka sace inda suka basu waya sukayi magana da iyalansu. “Babu tsangwama Bugu ko wani Cin mutunci ga iyalan namu ga yanda mukaji daga garesu a yanzu” inji wani da aka kamawa Mata kuma take hannun Barayin, saidai ya ce “Mu hankalin mu ba zai taba kwanciya ba saboda duk wanda yake cikin danginsa kuma sai yau gashi ance yana wajen masu garkuwa da mutane kuma su masu garkuwa komai suna iyayi akansu idan har basu samu abinda suka nema ba ai ba zamu taba samun kwanciyar hankali ba.” A karshe sunyi godiya ga Al’uma bisa tausayawa da kuma irin yanda suka damu sunata tayasu Addu’o,i. Sana sunyi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da ta damu da al’amarin kuma ta sanya tsatstsauran mataki domin ceto iyalan nasu.