Gwamnatin jihar Yobe ta sanya ranakun yau Litinin da gobe Talata a matsayin hutu domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar.
Shugaban ma’aikata na jihar, Garba Bilal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu .
Shugaba Buhari zai ziyarci jihar ne domin kaddamar da wasu ayyuka da su ka hada da filin jirgin sama na jiragen kaya, kasuwar zamani da kuma cibiyar kula da lafiyar mata da yara.
A cewar Bilal, Gwamna Mai Mala Buni ya ayyana ranar hutun ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a damar tarbar shugaban da zai kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar.
“Na rubuta ne domin sanar da ku cewa mai girma Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya ayyana ranakun Litinin 9 da Talata 10 ga Janairu, 2023 a matsayin ranakun hutu,” in ji sanarwar.
“Wannan shine don baiwa ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a damar tarbar shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, wanda zai ziyarci jihar domin ziyarar aiki ta kwana daya.”
Ya bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su koma bakin aiki a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu.