Zaharaddeen Mziag @Katsina City News11/11/2022
Gwamnatin tarayya tace ba zata yarda ta bar kafafen sada zumunta na zamani ba, su jefa ƙasar cikin ruɗani ba. Ministan yaɗa labarai da Al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka a wajen wani shiri na nuna Nasarorin da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu tun daga shekarar dubu biyu da sha Biyar 2015 zuwa 2023 da aka gudanar karo na uku, a Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa shirin ya gudana a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta shirya na da nufin nuna nasarori da Gwamnatin ta samu na tsawon shekaru bakwai na wa’adin mulkinta, haka kuma shirin ya gayyato ministan Sufuri na jiragen sama, sanata Hadi Sirika, inda ya bayyana Ire-iren nasarori da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu a ma’aikatar tasa. Alokacin da yake jawabi na bude taro lai Muhammad yayi gargadi ga kafafen sada zumunta na zamani, duba da yanda suka yada labarai na ƙanzon Kurege da kuma yanda suke amfani da kafafen wajen cin mutuncinn Al’umma a faɗin ƙasar.