Gwamnatin tarayyar Nigeria karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da sabuwar manufar gwamanti a kan Harsunan gida.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar shugaban Kasa ta Asa Rock yau laraba 30/11/2022 Jim kadan bayan Kammal a taron majalisar zartaswa ta kasa, Ministan Ilimin tarayyar Nigeria Mal Adamu Adamu ya ce, Majalisar zartaswar a zamanta na yau ta amince da kudurin Qasa a kan harsunan gida Wanda a karkashin wannan sabon kuduri haramun ne koyar da yara yan firamare da harshen Ingilishi, maimakon haka tsarin ya tanadi a koyar da yara yan firamare tun daga aji Daya har aji shida da harsunan su .
Duk da ya ke ministam ya ce sun san aiwatar da wannan tsarin ba zai rasa fuskantar kalubale ba, amma dai ya ce nan gaba za a fitar da jaddawalin tsarin gudanarwar .
Da aka tambaye shi ko ya za a yi a inda yara su ka fito daga mabanbantan kabilu alhalin su na karatu a makaranta Daya? Sai ya ce a irin wannan yanayin harshen da ya fi rinjaye a wajen da shi za a yi amfani .
Kamin dai gwamantin Shugaba Buhari ta fito da wannan sabon tsarin da masana su ka dade su na kiraye kirayen a gudanar, Najeriya ta na kan tsarin koyarwa da harshen uwa ne daga matakin share fagen shiga firmare ( nursery) zuwa firamare aji uku . Amma yanzu idan aka fara aiwatar da wannan sabon tsarin zai kunshi har zuwa kammala firame .