Sanata Ahamed Babba Kaita Dantakarar Sanata daga shiyyar Daura ya bayyana cewa Gwamnan Katsina Aminu Masari zai fitar da Naira Biliyan ɗaya da Miliyan ɗari ɗaya, zaiyi amfani dasu wajen yaƙin neman zaɓen ɗan takararsa na jam’iyyar APC Dakta Dikko Raɗɗa.
Ahamed Babba ya bayyana cewa Gwamnatin Katsina zatayi Amfani da kananan hukumomi da suke fama da Matsalar tsaro a fidda kudin da sunansu.
Yace a ko wace ƙaramar Hukuma za a rubuta mata ambata Naira miliyan ɗari ɗaya ƙananan hukumomi goma sha ɗaya zasu sanya hannu abasu kuɗin daga bisani kuma amaidosu ace.
Ya bayyana cewa aidan har aka kawshi waɗannan kudin anyi amfani da jinin Al’ummar Katsina don yiwa wani Kamfe.
Yace idan Gwamnatin ta isa ta musanta hakan.
Sana ya zargi cewa za’a bawa Ciyamomin ƙananan hukumomi 34 Naira miliyan Sittin-sittin kowanne, sana kuma su rubuta sun amsa amma zasu maido naira miliyan arba’in-arba’in.
Ya kara da cewa, sana kuma akwai wasu Naira miliyan Arba’in-arba’in da za a basu kuma su rubuta sun amsa amma wannan ba zasu dauki ko sisin kwabo ba zasu maidosu, za’ayi amfani dasu ayiwa Tinubu Kamfen.
Babba ya bayyana cewa ba zasu sanya ido ana wulakanta Dukiyar Talakawa ba, ana tarawa jiha bashi. Yace “Yace Muna kira da Aminu Bello Masari, kada ya kuskura ya aikata haka” yace ko kuma muci gaba da bayyanawa Duniya duk wani motsinsu.
Kaita yace “Abinda muke fada gaskiya ne munsan Gwamnatin nan munsan Sirrinta bamu taba zuwa mukai maku karya ba, kuma ba zamuyi ba.” Don Allah yace idan har muka amshi Gwamnati sai ya biya kudinannan ba Gwamna yayi ba ko shugaban kasa yayi.
Babba Kaita ya bayyana haka a wajen taron yakin neman Zaɓen Sanata Yakubu Lado Danmarke a garin Daura ta jihar Katsina ranar Alhamis.