Kwamitin kula da tsaftar muhalli na jihar Kano ya rufe wani kamfanin sarrafa ƙarafa ta kasar China, YoungXing Steel da ke Kano a jiya Asabar bisa karya dokar tsaftar muhalli na wata-wata.
Haka kuma ta ci tarar kamfanin Naira miliyan 5.
Kotun tafi da gidanka ta kwamitin, karkashin jagorancin Alkali Auwal Sulaiman, ta ba da umarnin rufe Kamfanin tare da sanya tarar kamfanin YoungXing Steel.
Hakazalika, kotun tafi da gidan na ka tanci wani gidan mai, MAM Oil and Gas tarar dubu 500 saboda karya dokar ta tsaftace muhalli.
Daga baya shugaban kwamitin, Kabiru Getso ya shaidawa manema labarai cewa, kamfanin na kasar Sin, baya ga gudanar da aiki a lokacin dokar tsaftar muhalli, ya na kuma keta hakkin ma’aikatansa.
“Ma’aikatan ba sa saka kayan kariya na yayin da suke gudanar da aiki kuma su na aiki ne da manyan ƙarafa da za su iya kisa.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa aka rufe kamfanin kuma ba zai yi aiki ba har sai an samar da dukkan abubuwan da suka dace don kare lafiyar ma’aikata da kuma bin dokokin jiha jihar,” in ji Mista Getso.
Getso, kuma Kwamishinan Muhalli, ya yi kira ga sauran kamfanoni na kasashen waje da na gida da su daina karya dokar tsaftace muhalli ba tare da hakura ba.
Kwamitin ya kuma gargadi al’ummar Kano kan zubar da shara a kan tituna ba gaira ba dalili.