Gwamnatin Kaduna ta amince a mayar da malaman makarantar firamare fiye da duɓu ɗaya da ta sallama a Yunin 2022 bayan yi musu wata jarrabawar tabbatar da ƙwarewarsu.
Kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar Hajiya Hauwa Muhammad ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da aka fitar yau Laraba.
Hajiya Hauwa ta ce malamai 1,266 ne aka yi wa jarrabawar gwajin cancantar yayin da 22 a cikinsu aka tsame su daga jadawalin albashin gwamnati.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa a Yunin 2022 ne ma’aikatar ilimin ta kori malaman Firamare 2,357 saboda gaza tsallake jarrabawar.
Ita ma jaridar Punch ta ruwaito ma’aikatar ta yi bayanin cewa an sallami malamai 2,192 saboda ƙin rubuta jarabawar yayin da malamai 165 kuma aka kore su saboda rashin tabuka abin a zo a gani.
Wasu daga cikin malaman da matakin ya shafa sun yi ƙorafin cewa sun rubuta jarrabawar kuma sun ci kuma duk da haka aka kore su yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa ba su da lafiya a lokacin da aka yi jarabawar kuma sun gabatar da takardar shaida.
Su kuwa wasu malaman cewa suka yi an yi garkuwa da su ne a lokacin, yayin da wasu suka ce a lokacin an dakatar da su ne saboda aikin tantance takardunsu.