Ginin titin saman da aka fara a Shataletalen hanyar GRA da aka kaddamar a watannin baya, Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal ne ya bayyana yanda aka raba diyya ta hanyar takardar karbar kudi a banki wato Cheque ga wadanda abin ya shafa wanda aka gudanar a Sakatariyar karamar hukumar Katsina, Sakataren Gwamnati wanda mukaddashin Babbann sakataren a bangare a bangaren harkokin Siyasa Alhaji Suleman Kankia ya wakilta ya bayyana cewa aikin ya shafi mutane dari da biyar ne a wajen. Darakta kasa da Sufiyo a ma’aikatar Alhaji Mustapha Zubairu ya bayyana cewa, anbi kyakkyawan tsari a wajen rabon kudin. A jawabin su daban-daban shugaban ƙaramar Hukumar Katsina wanda shugaban sashen mulki na ƙaramar hukumar Alh. Mustapha Idris ya wakilta, tare da wakilin mai martaba Sarkin Katsina, sarkin Dawa Alhaji Abba Balarabe, sun yabawa Gwamnonin jiha bisa gudanar da Aikin akan hanyar da ta dace, da kuma raba kudin diyyar akan wadanda abin ya shafa.