Gwamna Masari na Katsina zaiyi hadin gwiwa da makarantar Al’raqib Acadamy karkashin jagorancin Alh. Sanusi wada Domin bawa marayu da Jawara da harin ‘Yanbindiga ya rutsa dasu Ilimi kyauta.
Yarjejeniyar zata kasance da hukumar UNDP domin koyar da marayun Ingantaccen Ilimi. Gwamnan yayi kira da hukumar makarantar da ta shigo da daidaikun jama’a da kungiyoyi don su taimaka wajen samar da gine-gine da kayayyakin koyarda sana’o,in hannu ta yadda za a dunga koyar da Matasa Maza da Mata a bisa tsarin Musulunci.
Haka zalika Gwamnan yayi alkawarin gina hanya a sashen Sakandire da zata zagaye Makarantar a lokacin da shugaban kwamitin amintattu Alh. Khalil musa kofar Bai yake zagayawa da Gwamnan a harabar makarantar, yake fadamashi cewa Alhaji Sanusi wada shi kadaine ya gina makarantar. A karshe Khalil kofar bai yayi godiya ga Gwamnatin jihar katsina a karkashin Jagorancin Rt.hon Aminu Masari