Gwamnan jihar Katsina ya bayyana bukatar ganin masu iko na taimaka ma masu ƙaramin ƙarfi a cikin jihar.
Aminu Bello Masari ya faɗi hakan ne a lokacin kaddamarwa da kuma raba kayan aikin asibitin ƙashi dana sauran asibitoci, litattafan karatu, kekunan tura marasa lafiya guda 100, da sauran kayan kula da lafiyar yara da gidauniyar tallafa ma al’umma mai suna Aminu Masari Foundation hadin gwiwa da kungiyar Bruderlife suka shirya kuma ya gudana a dakin taron shugaban kasa da ke gidan gwamnatin jihar Katsina.
Ya ce gidauniyar da aka assasa kimanin shekaru 18 da suka gabata, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimaka ma mabuƙata masamman ma akan abubuwan da suka shafi ilimi da makamantansu.
A nashi ɓangaren, shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar Kabir Mashi wanda ya samu wakilcin mataimakinshi Abdullahi Imam ya yi kira ga mutanen da ke da niyyar bada gudunmawarsu zuwa ga mabuƙata da su bada ta ta hanyar gidauniyar.
Tunda farko a jawabinshi sakataren gidauniyar Ibrahim Ahmed Katsina, ya ce gidauniyar na gudanar da ayyukan taimakon al’umma daban daban da suka shafi aikin idon da aka yi ma kimanin mutane 100 a fadin jihar Katsina a baya.
Ya ce hakan dai kari ne ga taimakon kiwon lafiya da aka ba mutane 3,000, inda yake mai bayyana cewa a kwanakin baya ma gidauniyar ta taimaka ma mutane masu bukata ta masamman da kekuna 200.
Itama da take magana, ma’assasiyar kungiyar Bruderlife Mrs. Merry Bruder ta yaba ma gidauniyar Masarin bisa yin haɗin gwiwa da su, tare da aiwatar da shirye shirye masu amfani ga rayuwar al’ummar jihar Katsina.
Hakanan kuma, ta yaba ma uwar gidan gwamnan jihar Katsina Zakiyya Aminu Masari bisa taimakon da ta ke ba kungiyoyi masu zaman kansu don ganin sun yi aiki a jihar.
Shugaban hukumar gudanarwar Asibitin Katsina Dr. Abduljalal Umaru Abdullahi da kuma mai ba gwamna shawara akan masu bukata ta masamman Ya’u Rufa’i Zakka sun yi alkawarin yin amfani da kayan yadda ya dace.
Hakanan kuma mai ba gwamnan shawara ya bukaci gwamna da ya hanzarta amincewa da kudirin dokar kafa hukumar gyare gyare wanda yanzu haka ya ke gaban majalisar dokokin jihar.