Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse daga yau Lahadi.
Hakan ya biyo bayan amincewar kwamitin mutane bakwai na masu naɗa Sarki a masarautar Dutse, inda su ka zaɓi Muhammad Hameem a matsayin sabon Sarkin Dutse da dukka kuri’u bakwai a cikin ‘yan takara uku da ke neman kujerar sarauta.
Nadin dai ya zo ne ƙasa da kwanaki bakwai da rasuwar Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sanusi.
An tattaro cewa, daga bisani an mika wannan amincewa ga majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, wacce ita ma ta amince da matakin da masu naɗa Sarkin su ka ɗauka.
Sanarwar ta ce Majalisar Sarakunan ta aike da sunan Muhammad Hameem, wanda ɗan marigayi Sarkin Dutse ne, da sauran ’yan takara biyu zuwa wajen neman amincewa.
A cikin sakon fatan alheri ga sabon sarki, Gwamna Badaru ya taya sarkin murna tare da yi masa fatan Allah ya shiryar da shi, da hikima da kuma kariya a tafarkinsa.