• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai

December 22, 2022
in Sashen Hausa
0
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai
0
SHARES
20
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Daga VOA Hausa 21/12/2022 ✍️

A karo na biyu jiya Talata gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sake kin amsa gaiyatar Majalisar wakilai a bisa hujjar cewa bai dawo daga kasar waje ba.

ABUJA, NIGERIA —

Tun a ranar !5 ga wanan wata ne Majlalisar ta aike wa Emefiele da gayyata domin ya kara yi masu bayani akan manufar bankin kan sauya fasalin kudin kasar ciki har da takaita yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun bankuna , amma zaman bai yiwu ba saboda an aike wa majalisar wasika cewa Emefiele ba ya kasar.

Haka a zaman na jiya talata ma, wasika ce mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan Babban Bankin kasar, Edward Adamu aka aika da ke cewa Emefiele bai dawo kasar ba har yanzu.

Wanan ya sa masanin harkokin diflomasiya da zamantakewan dan Adam kuma malami a Jami’ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk, ya yi nazari cewa dole ne Emefiele ya ji tsoron fuskantar Majalisa domin bai tuntubi Majalisar ba kafin ya dauki matakin da ya dauka akan sauya fasalin kudi da kuma yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun banki.

Farouk ya ce akwai badakalar da ake ta bincike akan sa saboda haka zai ji tsoron fuskantar Majalisar.

Shi kuwa kwararre a fanin tattalin arziki Ahmed Iliyasu Sardaunan Misau yana ganin ya kamata Majalisa ta ciza ta hura tunda an bada hujjar rashin zuwan Emefiele. Iliyasu ya ce ya kamata Majalisa ta yi wa Emefiele uzuri.

Dan majalisa mai wakiltan Birnin Kudu da Buji a Jihar Jigawa Magaji Da’u Aliyu wanda shi ne ya kawo kudurin gayyatar Emefiele a gaban majalisar ya yi duba da abin da doka ta tanada

Magaji ya ce doka ta ba Emefiele dama ya nemi shawarar Majalisa kafin ya yi wani tsari da zai shafi kasa baki daya, amma bai taba zuwa wurin su ba.

Magaji yace yin haka ya karya dokar kasa da kuma dokar da ta kafa babban Bankin kasar..

Majalisar ta sake ba Emefiele dama ya bayyana a gaban ta a gobe alhamis, abin jira a gani shi ne ko hakan zai yiwu

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

Majalisar dokokin jihar Katsina ta amince da kasafin kudi N289,633, 257,963 na shekara ta 2023.

Next Post

2023: Kotu ta tabbatar da hukuncin korar Al-Mustpha da wasu ƴan takarar AA

Next Post
2023: Kotu ta tabbatar da hukuncin korar Al-Mustpha da wasu ƴan takarar AA

2023: Kotu ta tabbatar da hukuncin korar Al-Mustpha da wasu ƴan takarar AA

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In