Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar duba aikin sabuwar hanyar da ta tashi daga Kofar Guga zuwa unguwar Masanawa dake nan cikin birnin Katsina.
Wannan aiki wanda ya shafi rusau na wasu gidaje da awon hanyar ya shafa, an fara shi ne bayan kammala biyan kusan Naira Miliyan Dari Hudu (N400,000,000.00) a matsayin kudin diyyar gidajen. Tuni dai an fara fitar da hanyar da gina magudanun ruwa.

Ziyarar Gwamnan Katsina Aminu Masari a Unguwar Sullubawa wajen Duba aikin Titin
Kamar yadda ya saba, Gwamna Aminu Masari yayi amfani da wannan damar domin sada zumunci, a inda ya ziyarci wasu fitattun dattawa da suke a wannan unguwa, watau Alhaji Usman Sarki da kuma Alhaji Ayuba Sullubawa. Haka kuma ya tattauna da al’umma, musamman wadanda za su ci gajiyar wannan aiki.
Yadda Gwamnan ya taka da kafar shi tun daga bakin Kofar ta Guga har ya zagayo ya bullo bakin Gidan Yari da kuma yadda al’ummar wannan yanki suka tarbi Gwamnan tare da yi mashi addu’o’in fatar alkhairi da gamawa lafiya, ya kara tabbatar da cewa ba shi da kyamar al’ummar shi, yana tare dasu suma suna tare dashi.
Ya Allah Ka iya mana, Ka amsa mana addu’o’in mu kuma Ka share mana hawayen mu.
