Gwamna Masari ya ƙaddamar da kwamitin miƙa mulki ga sabuwar Gwamnatin zaɓaɓɓen Gwamna Dr. Dikko Raɗɗa
Gwamna Aminu Bello Masari ya kaddamar da kwamitin miƙa mulki ga sabuwar Gwamnatin jihar Katsin, ƙarƙashin jagorancin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar, Dr. Dikko Raɗɗa.
A ranar 18 ga watan maris aka gudanar da zaɓen Gwamna a jihar Katsina wanda Dr. Dikko Raɗɗa ya lashe zaɓen ƙarƙashin jam’iyyar APC, Za’a kuma miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana.
Sakakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal shine zai jagoranci kwamitin miƙa mulkin mai membobi 40 sai kuma Kwamishinan Ruwa da albarkatu Honorable Musa Adamu Funtua shine zai jagoranci kwamitin shirye-shirye da tsare-tsare, wanda dake ɗauke da membobi 43.
Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar, Masari ya kira ga Kwamitin da suyi aikin tukuru don ganin an cimma nasarar miƙa mulki kamar yanda aka tsara.
Sannan ya roƙi Allah da ya ba kwamitin damar aiwatar da aikin sa don al’ummar jihar Katsina su cigaba da cin gajiyar mulkin jam’iyyar APC dake tabbatar da rokon demokradiyya.