Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da tabbatar da Alhaji Muntari Lawal Katsina a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, haka kuma ya aminta da nadin Alhaji Bature Umar Masari a matsayin Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jiha.
Dukkan nadenaden sun kama aiki ne nan take. An bawa Alhaji Muntari Lawal sakataren riko ne bayan da tsohon sakataren gwamnati Mustapha Muhammad Inuwa ya aje, domin takarar tsayawa takarar gwamnan Katsina a karkashin jam’iyyar APC da bai samu narasara ba.

Source:
Katsina City News