Wannan makaranta wasu bayin Allah suka assasata domin marayu da diyan ‘yan gudun Hijira suyi karatun firamare da Sakandare mai inganci kuma kyauta. Gwamnatin Jiha ita ma ta bada tata gudummawa wajen ganin makaranta ta tabbata.
Alhaji Muhammad Sanusi Wada (Rahusa Ventures) yake jagorantar wannan muhimmin aiki mai tarin lada, kuma shi ya zagaya da Gwamnan tare da yi mashi bayani kan tsarin wannan makaranta.
Muna rokon Allah Shi inganta.
Source:
Abdulhadi Ahamad Bawa
Via:
Zaharadeen Mziag