Daga Muhammad Kabir Taskar Labarai
An gabatar da Fai-fain Bidiyo Mai tsawon minti goma Sha bakwai Na Nuna ma al’ummar Jahar Katsina Irin Kyawawan Halaye Da Ayyukan Da Dan Takarar Gwamna a Karkashin Jam’iyyar APC Dr Umar Raɗɗa Yayi.
Da Yake Magana A Wajen Taron, Shugaban Gwagware Media Reporters Alh Isa Mukidad Yace “Wannan Kungiya Ta Gwagware Media Reporters Dr Dikko Umar Raɗɗa Ne Ya Assasata, tun Yana Shugaban hukumar bunkasa kanana da matsakaitun sana’o’i.
Mukdad Ya Kara da Cewa sunga ya kamata suyi Wani Abu ta yadda Zasu nuna ma Mutane irin Aikace-aikacen da Dr Dikko Umar Raɗɗa Yayi.
Yace “Dan Takarar mu mutum ne Mai Nagarta, Mai kwarewa, Kuma jajirtacce Wanda Yayi A Baya aka Gani”.
“A wannan Karni da Muke a ciki An wuce siyasar wane Kaza wane Kaza, Aa sai dai mikayi a Lokacin da kake da dama, da wannan ne za’a Gane mekayi, Kuma a doraka a Bisa mizani.
Daga karshe ya gode ma mahalatta Taron da waɗanda Suka Bada Gudummuwa don ganin wannan taro ya wakana.
Shima a nashi Jawabin Ɗan Takarar Gwamnan Dr Dikko Umar Raɗɗa Ya yaba da irin Na Mijin kukarin da Kungiya Gwagware Media Reporters su kayi.
Yace Sunyi Abinda Ya Kamata domin sun Nuna kwarewa na Aikin Jarida. Sana ya Kara da Cewa “kukalli kanku Cewa zaku Iya gogaiya da ko waɗanne Yan midiya na Kowane sashe a kasar Nan.
Dan takarar ya Kara karfafa masu guiwa Cewa su cigaba da irin yadda Suke. ba zagi ko Cin mutunci iyaka idan an taɓa Ku, ku cigaba da fiddo ayyuka kuce Suma su fiddo da Nasu.
An Gudanar da Taron ne a Babban Dakin taro na katsina motel
13/11/2022