Shahararran Jarumin fina finan Hausa Mustapha Naburiska a wata tattaunawa da DCL Hausa Yace tallan da wasu mawaka keyi na Dr Nasiru Yusuf Gawuna Akwai mugunta al’amarin Mustapha na buriska Yana magana ne kan wakar da mawaki Rarara ya fitar kwana’kwanan nan wacce Yayiwa Gawuna Mai taken Girmanka Akwatinka.
A jawabin sa Naburiska Yana cewa Maganar Gaskiya tallan da wa’yan nan mutanen da suka dawo sukeyi Akwai mugunta ta yaya za’ayi Waka ace girmanka Akwatin ka? Kenan duk wanda Bai iya kawo Akwatin sa ba kenan ba za’a iya bashi mukami ba duk wahalar da yayi?
Har ila yau Naburiska ya koka ga yadda mawaki Rarara ke zagin wasu manyan jihar Kano na Siyasa a cikin habaicin Waka inda yace ya za ayi ace yau ka zagi Mista A gobe Kuma ka zagi Mista B?