
Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Alh Aminu Bello Masari ya fadi hakan ne a yau, lokacin da ya karbi bakuncin Jailani Aliyu, Shugaban Hukumar Kera motoci na Kasa a ofis nashi dake gidan Gwamnatin Jiha.
Alh Aminu Bello Masari ya cigaba da cewa abisa wannan ne yasa Gwamnatinshi ke kokarin zakulo matasa masu baiwa ta musamman domin nuna su a idon duniya, wanda, idan baa mance ba a irin wannan shiri na gasar zakulo matasa masu baiwa ta musamman wato “Katsina National Talent Hunt Challenge” da ya gabata a shekarar da ta gabata, aka samu wasu yara da sukai zarra, inda yanzu haka suna kasashen waje ta dalilin wannan. saboda haka a wannan karin ma gashi zaa gudanar da bada kyauta kashi na biyu a gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya, Gwamnati zata cigaba da kokarin tallafama matasan da irin baiwar da Allah ya basu, domin su zama wasu a gobe, saboda haka muna bukatar shugowar wasu daga gida da waje, domin ganin shirin ya dore.
Daga Karshe Maigirma Gwamna yayi godiya ga Jailani Aliyu abisa amsa gayyatar da Gwamnati tayi mashi, domin halartar bada kyautar shirin kashi na biyu.
Da yake Jawabi, Jailani Aliyu yayi godiya ga Maigirma Gwamna Masari abisa sake gayyatar shi da akai domin ya sake sheda bada kyautar kashi na biyu ga matasa masu baiwa ta musamman da suka shiga gasar Katsina National Talent Hunt Challenge da zaayi gobe idan Allah ya kaimu lafiya. Haka kuma ya nuna irin farin cikin shi abisa ziyarar da yakai a makarantar koyon Kimiya da fasaha ta Jiha da ya samu yara matasa suna koyon abubuwa da dama na kere kere, daga ciki akwai koyon aikin walda da kanikanci, wanda yace ta hakan ne suma zasu iya koya ma wasu a gaba, ya kuma yaba ma Gwamnati abisa irin yadda ta jajirci wajen gina matasa ta hanyar koya masu sana’o’in hannu wanda a yanzu sune ke rike da duniya.
Wadanda suka rufa ma Jailani Aliyu baya sun hada da Faisal Jafar Rafin Dadi, Mansur Kurfi, Alh Mannir Talba babban sakatare a hukumar koyon kimiya da fasaha, da kere kere, Alh Usman Babban Mataimaki na musamman akan tsaro, Arch Mustapha Maikudi Kankia, da yan wasu daga cikin ma’aikatanshi.
Daga ofishin Darakta Janar, Sabbin Kafafen Sadarwa na Zamani na Maigirma Gwamna.
15/2/2023.