Gidauniyar Dahiru Bara’u Mangal Foundation na cigaba da bada magani ga masu lalurar haniya da kuma lalurar fitsari a fadin jihar Katsina.
A ranar litinin 22/08/2022, Gidauniyar ta ziyarci asibitin kashi ta Katsina watau Amadi Rimi (Othorpedic Hospital).
Da yake yima manema labarai karin bayani jim kadan bayan ya ziyarci asibitin kashin, daya daga cikin mambobin Dan kwamitin amintattu na gidauniyar Hussaini Kabir ya bayyana cewa” wannan shi ne karo na biyu da Gidauniyar ta gudanar da aikin kula da marasa lafiya a cikin wannan shekarar da muke ciki ta 2022.
Ya kara da cewa” wannan aiki ya kunshi masu larurar haniya mutum 350, da kuma masu lalurar fitsari da masu lalurar Ido sama da mutum 1000 da su ka amfana da wannan aiki kuma aikin, wanda zai lakume sama da naira miliyan ashirin da biyar(25,000,000) kuma komi kyauta babu mai biyan ko sisin kobo.
Mobile Media Crew ta zanta da wadanda su ka amfana da wannan aiki, inda su ka nuna farin cikisu da yin godiya ga wanda ya assasa wannan Gidauniya, watau Alhaji Dahiru Bara’u Mangal. Daga karshe sunyi kira ga masu hannu da shuni suyi koyi da irin halinsa.