• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Gawuna Ya Taya Abba Gida-Gida Murnar Lashe Zaben Gwamnan Kano

Katsina City News by Katsina City News
March 29, 2023
in Sashen Hausa
0
Gawuna Ya Taya Abba Gida-Gida Murnar Lashe Zaben Gwamnan Kano
0
SHARES
6
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Matakin na zuwa ne mako daya da bayyana sakamakon

Bayan mako daya da bayyana sakamako, dan takarar Gwamnan Jihar Kano a jamiyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, ya mika sakon taya murna ga zababben Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf.

Gawuna wanda kuma shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar ya mika wannan sakon ne a cikun wani faifan murya da Mataimakinsa kan harkokin Watsa Labarai, Hassan Musa Fagge ya fitar ya aike wa Aminiya.

Sakon na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba Abba na jam’iyyar NNPP shaidar lashe zaben a Kano.

Gawuna ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne duba da cewa duk da korafin da suka yi wa Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Kasa kan ta sake bibiyar zaben amma a maimakon hakan sai ta bayar da shaidar cin zabe ga dan takarar Jamiyyar NNPP.

“Kowa na sane da cewa mun rubuta wa Hukumar INEC korafinmu akan zaben da aka gudanar ranar Asabar 18 ga Maris, wanda muka nemi ta sake gudanar da zabe a wasu wutare da wadancan abubuwa suka abku sabanin sanarwar da ta bayar cewa dan takarar Jamiyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben, amma sai ga shi a yau 29! ga watan Maris Hukumar INEC ta kara tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben ta hanyar ba shi takardar shaidar lashe zabe”

Gawuna ya yi kira ga magoya bayansa da su karbi kaddara.

“Dama tun a baya mun sha fadi cewa idan lamarin nan alheri ne Allah Ya ba mu idan kuma ba alheri ba ne to muna rokon Allah Ya canza mana da mafi alheri.  Don haka nake kira ga magoya baya da su zama masu karbar kaddara”

Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri tare da yin adduar Allah Ya sa ya zama shugaba mai adalci.

“Muna yi wa wanda Allah Ya ba wa adduar Allah Ya sa ya zama shugaba nagari mai yin adalci ga kowa. Allah Ya sa mu kuma mu zama masu biyayya ga shugabanci”

Share

Related

Source: Aminiya
Via: Katsina City News
Previous Post

Akwai ’Yan Siyasar Da Ke Kokarin Hana Rantsar Da Tinubu – DSS

Next Post

Dakta Dikko Umar Radda ya gabatar da kwamitocin da zasuyi bitar Kundin Manufofin Gwamnatinsa…

Next Post
Dakta Dikko Umar Radda ya gabatar da kwamitocin da zasuyi bitar Kundin Manufofin Gwamnatinsa…

Dakta Dikko Umar Radda ya gabatar da kwamitocin da zasuyi bitar Kundin Manufofin Gwamnatinsa…

Recent Posts

  • Nigeria Loses 965 Soldiers, Policemen To Boko Haram, IPOB In 2 Years
  • Gbajabiamila ya gode wa Tinubu bisa naɗa shi shugaban ma’aikata
  • Tinubu ya jajanta wa Indiya kan hatsarin jiragen ƙasa
  • Hajj 2023: Azman begins airlift of pilgrims Today
  • Hajj Airlift: NAHCON Airlift 14,000 pilgrims in 33 flights operations, set up back up plans

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • June 2023
  • May 2023
  • April 2023
  • March 2023
  • February 2023
  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • English
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Interview
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Press Release
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Sashin Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.