…Ta tabbata ba su da mutane
Inji Shafi’u Duwan
@Katsina City News
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Mani, kuma jigo a cikin zababbun shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Katsina, Alhaji Shafi’u Duwan, ya tabbatar da cewa gaskiya ta bayyana a taron da jam’iyyar PDP ta gudanar jiya Talata, ta nuna iya karfinta a Jihar Katsina.

Alhaji Shafi’u, wanda ke magana da Editan jaridun Katsina City News ya ce; “Taron da PDP ta yi sun kira shi da babban taro na amsar wadanda suka canza sheka da kuma kaddamar da kamfen na Gwamna a Katsina, kuma taron yakin zaben dan takarar Shugaban Kasa, amma ya filin taron Karakanda ya kasance?”
Alhaji Shafi’u Duwan, wanda yake cikin fitattun ‘ya’yan jam’iyyar APC a Jihar Katsina, ya ci gaba da cewa, filin ya zama kamar ka raba shi hudu ne, sai mutanen su rabe a bangare guda, yayin da sauran kashi ukun babu kowa.

Ya ce; “Na bi duk taron a kafar yanar gizo ta Katsina City News da Jaridar Taskar Labarai da suka kawo taron kai tsaye. Lokacin da nake kallo na yi dariyar farin ciki da godiya ga Allah cewa har yanzu Katsina Jihar ta APC ce.”
Alhaji Shafi’u ya ce; “Na ji lokacin da DG na kamfen din Mustafa Inuwa a jawabinsa a wajen taron ke bayanin cewa, wai mutane sun gaji da jira ne, saboda matsalar tsaro a yankunansu suka yi tafiyarsu.”
Ya kara da cewa; “Wannan ya tabbatar wa da kowa cewa ko su sun tabbatar da cewa babu jama’a a taron.”

Alhaji Shafi’u ya kara da cewa, kuma mutanen Katsina sun tabbatar da cewa mafiya yawan wadanda suka je wajen taron baki ne daga jihohin makwabta. “Bayan taron an gan su sun kuma hanyar komawa jihohin su,” ya jaddada.
Alhaji Shafi’u ya kara da godiya da al’ummar yakin Daura, a kan yadda suka fito suka yi wa dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC, Dakta Umar Radda tarba ta daraja da mutunci da shan alwashin bai wa jam’iyyar APC kuri’unsu a duk zabubbakan da ke tafe a yankin nasu.
Duwan ya kara da cewa Dakta Dikko Umar Radda ya rika bi duk mazabun unguwani a kowace Karamar Hukuma. Sun gan shi, ya gan su, ya san matsalarsu, kuma ya sha alwashin dora wa daga duk ayyukan alherin da gwamnatin APC take gudanarwa.
Alhaji Shafi’u ya kara da cewa yana da kyau mutanen Katsina su kara sanin waye Yakubu Lado Dan Marke, dan takarar Gwamnan Katsina a jam’iyyar PDP, kuma wane ne Dakta Dikko Umar Radda dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC.
“Duniya da kuma kasarmu Nijeriya na cikin wani yanayi na matsalar tattalin arziki, wa zai fitar da Jiharmu ta Katsina daga wannan kangin?
Amsa da karfin ikon Allah da taimakon Allah, babu kamar Dakta Dikko Umar Radda,” ya karkare.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com