Bayan Kaddamar da yaƙin neman zaben takarar Gwamnan jihar Katsina a jam’iyyar APC dakta Dikko Umar Raɗɗa da Gwamna Masari yayi a garin Faskari Ranar Litanin 5 ga watan Disamba, tawagar yaƙin neman zaben Ɗantakarar Dakta Dikko Radda ta mazaya shiyyar Daura inda suka fara shiga Lungu da saƙo na kananan hukumomi domin gabatarwa, kaddamarwa da kuma Tallata manufofin Ɗantakarar domin jama’a su zabeshi a matsayin Gwamnan jihar Katsina na shekarar 2023. Inda suka fara da karamar hukumar Ɓaure, Zango da Mai Aduwa.
Ayau juma’a jirgin yakin neman zaben ya shiga garin Mai adawa da kuma mazaɓunta domin cigaba da yakin neman zaɓen inda Dakta Dikko Umar Raɗɗa da sauran ‘Yan tawagar sa, Daraktan yaƙin neman zaɓe Artc. Ahamad Dangiwa shugabannin jam’iyya da sauran yan kwamiti suka cigaba da shiga lungunan ƙaramar hukumar Mai Aduwa, da Unguwannin Dagatai dake faɗin ƙaramar hukumar.