Babban kalubalen da shugabanni ke fara fuskanta bayan cin zabe shi ne na kasa banbancewa tsakanin wadanda su ka taimake su su ka ci zabe da kuma wadanda za su taimake su sauke amanar da talakawa su ka dora ma su.
Kowanne da irin baiwa da hikimar da Allah ya yi ma shi. Wani Allah ya ba shi hikimar mobilising mutane a samu nasarar zabe. Wani kuma Allah ya ba shi rikon amana da hikimar gudanar da aiki. Wasu Kuma Allah ya ba su duka
Wadansu su kan yi kuskuran daukar mukaman gwamnati a matsayin ganimar yaki. Wannan ya kan sa su dauki mukaman da aka ba su a matsayin wata hanya ta more rayuwa da gina kan su. Domin ita ganima, lada ce bayan gama aiki. Amman shi mukamin gwamnati kuwa, amana ce domin gudanar da aiki ga al’umma…
Wannan kasa banbancewa tsakanin ganima da kuma ba da amana, na daya daga cikin manyan dalilan da ke sa gwamnatoci kasa cika alkawurran da su ka daukar ma talakawa..