• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Ganawa Da Yan Takarar Gwamnoni A Katsina: Kowane Dan Takarar Ya Fede Kudurorinsa Tun Daga Biri Har Wutsiya. 

January 15, 2023
in Sashen Hausa
0
Ganawa Da Yan Takarar Gwamnoni A Katsina: Kowane Dan Takarar Ya Fede Kudurorinsa Tun Daga Biri Har Wutsiya. 
0
SHARES
32
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Muhammad A. Isah

A taron zauren jama’a da aka gudanar, na ganawa da ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina a ranar Asabar 14 ga Janairu, 2023, don jin kudurori da aniyar da suke da ita ga al’ummar jihar katsina da za su aiwatar da zarar Allah ya ba wa mai rabo sa’a a cikinsu na darewa kan kujerar gwamnan jihar ta Katsina, daukacin ‘yan takarkarin sun yi filla-filla da kudurinsu a gaban bainar al’ummar jihar Katsina.

Taron ganawar wanda rukukun gidajen yada labarai na Media Trust da CDD hadin gwiwa da Katsina City News, Vision Fm da Gidan Talabijin na Farin wata suka shirya, ya samu halartar dubban mutanen jihar Katsina wadanda suka hada da kungiyoyin dalibai da sauran al’umma, ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, masu fada-a-ji, ‘yan kasuwa, jami’an tsaro da kuma ‘yan jaridu.

Taron dai an soma gabatar da shi ne da misalin karfe 10:00 na safe a dakin taro na hukumar kula da kananan hukumomin jihar katsina da ke kan hanyar zuwa karamar hukumar Kaita.

Farfesa Sani Abubakar Lugga shi ne uban taro, kuma shi ne ya soma da gabatar da jawabi a taron, in da ya hori ‘yan takarar da cewa su ji tsoron Allah a yayin gudanar da mulkin al’umma, sannan su kuma yi aikin da zai kawo ci gaba mai dorewa ga al’ummar jihar ta katsina.

Shu’aibu Mungadi dan jarida mai sharhi kan al’amurran yau da kullum daga gidan talabijin na farin wata, shi ma a nashi jawabinsa ya ja hankalin ‘yan takarkarin da cewa su tabbatar sun bayyana tare da zayyano kudurori wadanda za su iya aiwatarwa idan sun cimma gaci, domin muddin wani dan takara ya ‘ki aiwatar da kudurin da ya fadi ga mutanen wannan zaure, to fa mu ‘yan jaridu mun taskace su, kuma za mu ci gaba da zakulo su mu yi ta fadawa al’umma, domin kuwa baki shi ke yanka wuya.

Samar da Tsaro, habaka harkokin kasuwanci, inganta noma, samarwa matasa aikin yi, tsari na musamman ga Iyaye Mata, ababen more rayuwa, inganta hanyoyin sufuri, inganta harkar koyo da koyarwa, kawo kwararru a fannin kimiyya da fasaha su ne muhimman kudurorin da ‘yan takarkarin sukai ta kai-komo wajen bayyanarwa a zauren taron.

Abin da muka lura da shi a wajen shi ne, ‘yan takarar sun yi iya kokarinsu wajen kare muradan da suka zayyano musamman a yayin amsa tambayoyi mahalarta. Sai dai a yayin tattaunawarmu don jin ra’ayin mahalarta kan wanda suka fi gamsuwa da kudurorinsa, sun fi bayyana mana wasu kadan daga cikin ‘yan takara da cewa su ne suka fi kawo kudurori bisa tsari da kyau, kuma suka kare su bisa gamsasshiyar hujja da dalili a yayin amsa tambayoyi a zauren.

‘Yan takarkarin Gwamnonin daga jam’iyyu 7 ne suka halarci tattaunawar, wadanda suka hada da; Dr. Dikko Umar Radda daga jam’iyyar APC wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Faruk Lawal Jobe, Sanata Yakubu Lado Danmarke daga Jam’iyyar PDP, Injiniya Nura Khalilil daga jam’iyyar NNPP wanda ya samu wakilcin Dr. Muttaka Rabe Darma, Imrana Jino daga PRP, BUT da Malam Kabir Kofar Bai kewa takara, Dantakara Gwamna daga ZENITH LOBOUR PARTY, da jam’iyyar SDP Ibrahim Zakari Talba, da ya samu wakilcin mataimakinsa.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

Yan ta’adda sun kona limamin Cocin Katolika da ransa a jihar Neja

Next Post

Terrorists Shot Pastor, Kidnap 7 Women, 2 Children in Katsina

Next Post
ba mutane 39 aka sace a Katsina ba – Ƴan sanda

Terrorists Shot Pastor, Kidnap 7 Women, 2 Children in Katsina

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In