
A ranar Laraba 21 ga watan Disamba Shahararriyar kungiyar nan mai suna Support Groups mai fafutukar ganin Bola Ahamed Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya, a ƙarƙashin jagorancin Dakta Baffa Babba Dan’agundi Shugaban KAROTA na Kano da Mataimakinsa Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar Katsina Alhaji Ibrahim Masari, sun shirya wani taron gangamin gamayyar kungiyoyi a jihar Katsina, domin bayyana maƙasudi da manufofi gami da tsarin da suke da shi na tallafawa al’umma da kai tsaye, yanzu da bayan anci zabe ta hanyar fasahar zamani kamar yanda Dakta Dan’agundi ya bayyana a wajen taron.

Dan’agundi ya ce, “Mun zagaya kusan dukkanin jihohi na Arewacin Najeriya don gabatar da wannan shiri da ita wannan kungiyar ta bullo dashi, domin amfanin ‘Yan Arewa, kuma munga cewa bisa abinda muka gani Katsina tana da tsari mai kyau fiye da kowace jiha” yace “Tsarin shiga wannan ƙungiya kai tsaye ta hanyar fasahar Zamani na Yanar gizo inda muka saki takardar cikewa da ƙa’idoji na cikewa wanda ga duk wanda ya shiga zai gani, kuma za a kiraka kai tsaye aimaka tambayoyi ka bada amsa kamar yanda idan buƙatar Tallafi ya tasi za a kiraka kaitsaye shima,” ya kuma bayyana cewa Kungiyar zata cigaba da taimakawa ‘yan Arewa bisa tsarin da take dashi, ko bayan zaɓe saboda shi Bola Ahamed Tinubu bayarrabe ne, da suka dade bisa wani tsari da suke a yankin kudancin kasar na fasahar zamani don tallafawa al’umma, yace don haka ya bullo da wannan tsarin ga Arewa.
An gudanar da gagarumin taron a dakin taro na ma’aikatar kananan hukumomin dake kan Titin Kaita a garin Katsina, inda dimbin al’umma suka je suka saurara don ji da ganin yanda zasu iya shiga wannan ƙungiya.