Sharhin Jaridun Katsina City News
www.katsinacitynews.com
Jaridun Katsina City News sun tabbatar an kammala duk wani shiri na komawar Alhaji Mustafa Inuwa cikin jam’iyyar PDP ya kammala.
Muna da tabbacin an kiyasta kudin da za a kashe, kuma har Sanata Yakubu Lado Danmarke, dan takarar Gwamna a jam’iyyar PDP ya bayar.
Matsalar turjewar tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema, wani Attajirin cikin Katsina ya warware shingen.
Hatta matsalar Malam Mahadi Shehu, dan asalin Katsina mazaunin Kaduna, wanda yanzu yake tare da takarar Atiku Abubakar ita ma an warware ta.
Duk wata kofa ta sulhu da fahimtar juna tsakanin Alhaji Mustafa Inuwa da jam’iyyar APC a matakin Jiha da Tarayya, Mustafa Inuwa ya killace ta.
Ga alama ya yanke shawarar tafiya, kuma tafiya zai yi, wasu ‘yan ga-ni-kashenin matasan masu goya masa baya sun fara gaba.
Babbar matsalar da ke gaban jam’iyyar APC ita ce, shekaru bakwai da watanni ya yi yana rike da muhimmin mukami a gwamnatin.
A tsawon wannan lokacin, Mustafa Inuwa ya zama kamar Firaminista ne a cikin gwamnatin, babu abin da ya fi karfinsa, sai wanda bai sa kansa ba.
Ya kafa mutane, kuma mafi yawansu suna tare da shi dari bisa dari. Hatta zaben da aka yi na kananan hukumomi yana da ciyamomi da kansiloli nasa.
Bincikenmu ya tabbatar mana babu wani yaron Mustafa Inuwa da zai bar mukaminsa, ba kuma wanda zai ajiye takararsa.
Ba wanda zai bi Mustafa a bayyane, amma za su tsaya inda suke su yi aikin cikin gida.
Mun yi magana da masu rike mukamai da wadanda aka ba takara mutane tara a cikinsu, sun tabbatar mana cewa suna nan a APC da matsayin da suke a kai, amma suna tare da Ubangidansu.
Yaran Mustafa Inuwa da ke rike da mukamai akwai yiyuwar wasu daga cikinsu su rika taimakon tafiyar tasa da kudi da kuma bayanai.
Duk wanda ya kalli wata hira da Yakubu Lado ya yi aka dora a shafukan sada zumunta, inda a hirar ya yi maganar wasu kudi da aka tura wa kananan hukumomi da yadda aka ce su yi da kudin, wasu bayanan da ya yi gaskiya ne.
Tambaya, wa ya fada masa? Watakila Shugaban wata Karamar Hukuma, ko wani ma’aikaci a Ma’aikatar kananan hukumomi. Ya fada kai tsaye, ko ya fadi wa wani aka fada masa.
Daga maganganun Mustafa Inuwa kamar yana nuna da an fara taba masa yara, akwai sabuwar magana.
A irin wannan yanayi ya APC da gwamnatinta za su yi? Wannan shi ne, gaba Kura, baya Siyaki.
Wani lamarin da ke damun APC shi ne, dan takararsu na Gwamna ya yi wasu kurakurai a baya, wadanda yanzu suke masa fatalwa. Yana kara aikata wasu kurakuran yanzu haka. Ko a daren Juma’ar da ta gabata a wajen liyafar cin abinci dare ta karrama Alhaji Muntari Lawal, Sakataren Gwamnatin Katsina, Madugu Katsina, Magatakardan Hausa, nan ma an yi wani kuren da wasu a gefe suka dan yi tsokaci.
Kuma akwai kallon da ake masa, wanda ya kasa canzawa.
Wasu kuma na tambayar, me ya sa na kusa da shi a da, yanzu suke gaba-gaba wajen adawa da shi?
Wadannan hudojin a siyasa na cikin makaman da PDP ta tanada a kan APC idan guguwar siyasar ta taso.
Babu abin da bai mafita, ko APC ta samo mafitar?
Katsina City News
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar Taskar Labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The Links News
@ www.thelinksnews.com
07043777779.08137777245