…Canjin Sabbin Kuɗi: Laifin Emefele ne ba Buhari ba.?
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Da Sanyin Safiyar ranar Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa ‘Yan Najeriya cewa, “Za’aci gaba da amsar Tsohuwar Naira ɗari biyu, tun daga yanzu har zuwa 10 ga watan Afrilu watan 4.”
Dani da kai da ku da ke, duka faɗin Najeriya mun Yarda mun Natsu mun Amince, zamu dunga karɓa da Mu’amala dasu na tsawon wannan Lokaci da Shugaban ya ƙara da kansa.
Idan har Kotun Ƙolin Ƙasa wadda ake mata kirari (Daga ke sai Allah ya isa) zata yanke Hukumci, Shugaba ya take, shi kuma ya bayyana nashi Hukumcin kuma ayi Biyayya ga Hukumcin, to Kotunan Najeriya basu da wani Amfani, yakamata Shugaban ya naɗa Kansa a matsayin Babban Alƙalin Ƙasa.
A gefe guda kuma Don tsabar son zuciya, ƙin Allah, da yaudarar Talakawa, wai wasu (Musamman Gwamnoni) suke buɗa baki suna cewa ba laifin Buhari bane, Laifin Emefele ne.
Don haka sun makashi Kotu, Kotun da bata da Amfani.
‘Yan Najeriya mu daina Yaudarar Kammu, Emefele dai Yaron Jonathan ne, kuma Shalelen Buhari. Saboda Buhari ya gajeshi ne wajen Jonathan, kuma ya bashi gatanci da kulawa da cikakken Iko, ba don komai ba sai don wata Manufa wadda zan iya cewa itace wannan.
Idan ba haka ba ai yanada karfin iko na cireshi, kamar yanda yake da karfin ikon take Umarnin Kotu, amma bai cireshi ba. Kuma idan ya iya, ai bashi kadai ya iya ba, ba shi kadai ya sani ba, balle ace yana kawowa ƙasa cigaba da bunƙasa Tattalin arzikinta, babu abinda ke cikin gudanarwasa sai rusa Tattalin arzikin Najeriya, amma a ganin Buhari hakan yayi Daidai.
Don gaka daga wannan Hukunci da Buhari ya yanke ga Duk mai cewa ba laifin Buhari bane, wallahi ƙarya yake yasan laifinsa ne, kawai yana Raragefe ne, kuma zakuce na faɗa maku nan da watanni kaɗan idan ta kacame.
Kuma mu Talakawan Najeriya ba Taimakon mu akai ba don ance Muci gaba da amsar tsaffin kudi koda ma ace da naira dubu da ɗari biyar ɗin dama ɗari biyu da Buhari ya Amince a amsa. Saboda ai sun bayyana cewa kudin da ke yawo hannun Mutane tsaffi Tiriliyan uku ne, amma sun karɓi Tiriliyan biyu da ɗigo shida, mi yayi saura kenan? Sauran ko sun ɓace ko sun ruɓe ko anyi gobara gidan wasu kuɗin sun ƙone, da sauransu. Don haka lallai babu ko Sisi a hannun Mutane, to mi zamu dunga kashewa kenan.? Wannan Rainin wayo ne, a baka da dama a karɓe da hagu.
Don haka Gwamnoni ku daina raina mana wayo, Shugaban Ƙasa Buhari yayi amfani da Talakawa ya samu tsantsar Soyayya, a karshe ya sakamasu da Mummuna, ku kuma ba maganar Talakawa bace a gabanku, maganar Dantakararku itace gabanku.
Ina fata, ga Talakawan da ake Yaudara suyi tunanin nemawa kansu hanyar da ta dace, ba mai kwazazzabo da Rami ba.