Jarida Radio 📻
Ranar Talata ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta yi wa kasuwar musayar kudaden ketare ta bayan fage dake Zone 4 a Abuja ƙawanya, inda suka tafi da wasu daga cikin ‘yan chanjin.
Wasu da lamarin ya faru akan idon su sun ce jami’an EFCCn sun isa wajen ne da misalin 2:00 na rana, inda suka datse dukkan wata hanya da zata kai layin da ‘yan chanjin suke harkokinsu, wanda hakan ya kawo tsaikon harkoki a kasuwar da ke Zone 4 na tsawon kusan sa’a biyu
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumar ta EFCC bata kai ga cewa uffan ba kan wannan batu.
Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tashin farashin dala a kasuwanin bayan fage a Najeriya, wanda masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arzikin kasar ke alakanta shi da matakin da babban bankin kasar ya dauka na sauya fasalin takardun kudin kasar nan da watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa ta 2023.
Faruwar wannan lamari dai ya dauki hankalin al’umma musamman masu harkokin musayar kudade a Najeriya na fargabar rashin sanin yadda lamarin ka iya fadada zuwa wasu jihohin kasar.
Rahoton Ibrahim Aminu