Shugaban hukumar na EFCC Abdulrashid Bawa ya buƙaci haka a zauren majalisa lokacin da yake kare kasafin Ofishinsa na 2023 a Ranar Talata.
Abdulrashid Bawa ya ce yakan zai bada dama ga samar da Makaranta mallakin hukumar domin horas da ma’aikatanta. Bawa yace an ware naira Biliyan uku a kasafin kudin shekarar 2021na Aikin amma ba’a ware ko sisin kwabo ba a wannan shekarar. Shugaban hukumar ya bayyana cewa hakan zai kara bawa hukumar damar kula da ma’aikatan ta wajen yaki da cin hanci da sauran laifuffukan. Bawa yace za ya roki majalisar zartarwa ta ƙasa, domin fara ginin makarantar koyarwa da horas da jami’an ta, wanda yace zai laƙume naira Biliyan uku, kamar yanda ya bayyana hukumar ta bukaci kimanin Naira Biliyan hamsin domin gudanar da Ayyukan.