Ƙungiyoyin agaji da ke kula da killace shanu a jihar gujarat da ke yammacin Indiya sun saki dubban shanu don yin zanga-zangar adawa da rashin cika alkawuran da gwamnati ta yi na taimako.
BBC ta rawaito cewa bidiyon yadda shanun suka dinga kutsawa cikin gine-ginen gwamnati sun yaɗu kamar wutar daji a kafafen sadarwa.
Masu zanga-zangar sun yi barazanar ƙaurace wa zaɓen da za a yi a jihar idan har gwamnati ta gaza sakin kuɗaɗe.
Gujarat na daga cikin jihohin Indiya da ke fama da wata annobar cutar fata da ke jawo asarar shanu.
Kusan shanu 5,800 ne suka mutu, yayin da aka ƙiyasta cewa 170,000 sun kamu da cutar.
Al’ummar Hindu mafi rinjaye a ƙasar na girmama shanu saboda suna ɗaukar su a matsayin wasu ababen bauta, don haka jihohi 18 na ƙasar da suka hada da Gujarat suka haramta yanka shanun.
Ko a shekarar 2017, Gujarat ta tsaurara dokokin kare shanu ta hanyar sanar da cewa za a hukunta duk wanda ya yanka saniya ta hanyar yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Daga cikin cikas din da zanga-zangar ta jawo har da yadda dumbin shanu ke kara-kaina a kan tituna suna jawo cunkoson motoci.
A cikin kasafin kudinta na bana, gwamnatin gujarat ta ware dala miliyan 61 don gyara wajen ajiye shanu da sauran dabbobin da suka tsufa a jihar.
Masu kula da wuraren killace shanu, sun ce babu wani kudi da suka samu daga gwamnatin, suna masu cewa an cuce su.
Sun ara da cewa duk da irin wakilan da gwamnatin ta aika, babu wata maslaha da aka samu.
Jaridar Indian Express ta ruwaito cewa kusan shanu 1,750 daga cikin 450,000 da ƙungiyoyin jin ƙan ke kula da su ne suka fita zanga-zangar.
“Jihohin da jam’iyyar BJP ke mulki kamar Uttar Pradesh da Haryana da Madhya Pradesh da Uttarakhand ne ka bayar da tallafi.
Ko jihar Rajasthan ma tana bayar da rupee 50 kan kowace saniya. To me ya sa Gujarat ta gaza kula da shanun?” in ji Vipul Mali, sakatare janar na Gujarat Gau Seva Sangh – kungiyar da ke kula da shanun da lafiyarsu ya fada.
Rahotanni a kwanakin da suka wuce sun ce, shanun sun bazu a kan tituna da shiga gine-ginen gwamnati a yankuna da dama a Gujarat.
Masu zanga-zanga sun je wani ofishin gwamnati ɗauke da kashi da fitsarin shanu.
Ƴan sanda sun ce sun kama masu zanga-zanga 70 a yankunan Banaskantha da Patan da kuma Kutch.
A yanzu masu zanga-zangar sun yi barzanar ci gaba da yi idan har ba a biya musu buƙatunsu ba.