Muhammad A. Aliyu @Katsina City News
Wani Saƙon Sauti da Katsina City News ta samu ya jiyo yanda Dantakarar Gwamnan Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke yake Ɗuɗɗurawa Shugaban ‘Yansanda DPO na Ƙanƙara Ashariya.
Hakan baya rasa nasaba da wani hargitsi da ya faru a garin Ɗanmarke mahaifar Ɗan takarar Gwamnan, a lokacin da tawagar abokin karawarsa na jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa yaje yawon Kamfe.
Jam’iyyar APC tayi zargin yanda magoya bayan Sanata Danmarke suka kaima tawagar yakin Neman zaben Dikko Raɗɗa hari inda aka farfasa Motocinsu da raunata wasu, a lokacin da ita kuma ɓangaren PDP sukace Mutanen Dikko Raɗɗa ne da shigarsu cikin garin suka kama fasa masu duk wata bana da Alluna na Dantakararsu.
Sanata Yakubu Lado Danmarke yayi zargin An shiryawa Magoya bansa cin zarafi da sa hannun DPO na Karamar Hukumar Ƙanƙara.