- Wajibine, duk Da’irar da zatashiga Zageyen Maulidi tayi Rijista da Kwamiti, kuma sai tayi Tuta mai dauke da suna da Adireshinta.
- An kayyade lokacin Zagayen Maulidi daga Karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma.
- An amince Sha’irai zasu shiga Zagayen Maulidi bayan Kwamiti ya tantancesu, amma an haramta masu shiga da Mata.
- An haramta shigar Kauraye, daukar makami, buga knockout da shaye shaye ba, duk wanda yayi Jami’an tsaro zasu hukuntashi.
- An haramta masu DJ shiga Zagayen Maulidi.
- An haramta shigar masu kallo fesa turare ta kowane fuska.
- An haramta mummunar shigar da ta sabawa musulunci.
- An haramta Raye Raye, Jan fada ko maida raddi a lokacin Zagaye.
- An haramta kafa rufunan kallo gab da hanya.
- An umarci dukkan Da’irori da suyi Kwamitin tsaro, sannan dukkan masu aikin Sakai sai sun yi Rijista da babban kwamiti.
Duk wanda ya sabawa waÉ—annan dokoki za ya fuskanci fushin Hukumomin tsaro.
Allah ya sa ayi taro lafiya a tashi Lafiya, amin.
Sanarwa Daga Kwamitin Mauludi Na Jihar Katsina
Source:
Kwamitin zagaye
Via:
Katsina