Dr Dikko Umar Radda ya yi alqawarin wanda ba wa mata a jihar Katsina ingantaccen ilimi da sana’oin da za su dogara da kansu su tallafi iyalansu da ba su dama a madafun iko da tafiya tare da su don inganta rayuwarsu da ciyar da jihar Katsina gaba. Ta bakin maixakinsa Hajiya Zulaiha Dikko Radda. Daga Bilkisu Yusuf AliZa mu so mu ji taqaitacce tarihinkiNi sunan Hajiya Zulaiha Abdullahi Matazu mahaifina xan Matzu ne mahaifiyata ‘yar Dutsim-ma. An haife mu a Kaduna anan muka tashi. mahaifnmu mai kishin jihar Katsina ne sosai ,saboda haka da lokacin da muka isa shiga Sakandire sai ya dawo da mu gida Katsina.Na yi sakandire a GASS Kabomo. Na fara 1996 na kammala 2001.Bayan na kammalaa an yi min aure a shekarar 2001 . Muna da yara guda 7.Maigidana Alh Dikko Umar Radda mutum ne mai kishin karatun mata don haka bayan mun yi aure ya yarje min na ci gaba da karatu. Na fara Difloma a vangaren shari’a (law) a nan Aminu Kano collefe of Legal studies a Kano. Da na gama law sai ya kasance kuma mahaifina bai ba ni qarfin gwiwa ba a fannin shari’a ba, saboda yana cewa duk alkalancin da za a yi. ba a kan alqur’ani da sunna ba, to mutum wuta zai je. Wannan yasa na sauya vangare na koma BUK inda na yi advance difloma a public administration. Da na gama sai suka ba ni admission inda na yi Bsc a political science . Bayan da maigidana ya samu sauyin aiki a SMEDAN sai na koma jami’ar Gwagwalada da ke Abuha na yi digirina na biyu a public administration. Alhamdlillah A matsayinki na matar xan takarar gwamnan jihar Katsina wanne fata za kiyi da tanadi ga mata a alqawurwura da ki ke yi a wannan zagayen na neman su zavi MaigidankiDr Dikko Radda mutum ne da yake da tausayin mata. Yana son ya ga mata cikin walwala ba ya son ya gansu da wahala duk wanda yake mu’amala da shi yau da gobe zai yi shaidar hakan. Ko kan hanya yake tafiya indai zai ga mace da kaya a kanta to kuwa da kansa zai karva ya taimaka mata. Kullum yana cewa mata masu rauni ne ya kamata a tallafe su. Kin ga mai wannan tausayin ba yadda zai yi ya bar mata a wani hali na rahin jin qai.Haka duk inda ya ga mace mai rauni sai ya tallafa mata. Alhamdlillah ko a lokacin yana SMEDAN mata su suka fi alfanar tallafinsa saboda ya lura sune suke da rauni kuma sune in an tallafesu taimakon yake tafiya kai tsaye ga iyalansu. Dr Dikko mutum ne da yake son ganin mace ta tsaya da qafafunta don haka yake tsaye kan ilimin mata da ba su sana’a kuma na tabbata da Allah ya ba mu nasara a wannan mulkin zai bayar da gagarumar gudummawa a wannan vangaren. Don haka nima zan yi iyakar qoqarina na ga na ba shi haxin kai da tallafa masa ta vangarena don tabbatar da wannan qudirin nasa. Nima kuma ba wai zan zauna ba ne zan yi amfani da duk iyakar iyawata bisa hurumin da doka ta bayar na ga na tallafi matan nan musamman ma ta vangaren sana’a. Wadda take da sana’a za mu qarfafeta wadda muka tabbatar ta iya za mu ba ta dama ta koyawa wasu wannan sana’ar wannan shi zai qara tallafarta. Waxanda kuma ba su iya ba, su ma anan zai sa su koya sannan za mu ba wa duk wanda ya koya jaro don ci gaba da tafiyar da sana’ar. Haka a vangaren neman ilimi nan ma za mu tallafawa mata sosai saboda duk wani cigaba yana qarqashin ilimi. In uwa ta kasance mai ilimi za a tarar da ‘ya’yanta a nutse kuma za ta tsaya gun tarbiyya da ilmantar da ‘ya’yanta a gaba.A jihar Katsina akwai mata da aka kashe mazajensu ko aka raba su da muhallansu wanne tanadi ku ka yi musuAlhamdlillah maganar rashin tsaro mu mun je mun zagaya mun ga abubuwa da kanmu mun ga tashin hankali. A irin wannan rayuwar duk wahalar kan koma kan mata ne. Su suka fi shiga ruxanin kuma kada ki manta ciwon ‘ya mace na ‘ya mace. Wani gida da na je lokacin da matan ke ba ni lavarin abin da ya faru ban san lokacin da na ga ina hawaye ba.A bin tausayin wasu mazajen an kashe su. wasu matan ma ba su da tabbacin mazajen suna raye ko ba sa rayen. wasu ma a gabansu aka yi wa mazajen mugun kisa, ko uwa a gabnta a kashe xanta tana gani. Wannan abu ne marar daxi da ya kamata a duba kuma muna nan da burin tallafar ire-iren waxannan za mu xau nauyin karatunsu mu ba su ayyukan yi don dai su zo su tallafi iyalansu, ba za mu bari su shiga wani hali ba da yardar Allah.Sannan muna addu’a kan wannan rashin zaman lafiyar kuma abin da Dr Umar Radda zai fi mayar da hankali akai fatansa kowa ya koma inda yake a ci gaba da walwala da kwanciyar hankali in sha Allah da addu;a da taimakon Allah da jajircewa, Sabida mata duk inda aka je aka dawo kan mata abin yake qarewa.Ya batun ilimi wanne alqawari ku ka yi a wannan vangarenAbu ba farko da Maigidana na ya yi alqawari shi ne samar da ingantaccen ilimi musamman mata da matasa waxannan sune za su ci gajiyar wannan hovvasa da Dr Dikko ya yi. zai xauki malaman makaranta a koya musu sababbin hanyoyi na koyar , za a yi musu training a matakai daban-daban. , malaman kuma za a ware lokaci da za’ayi musu bita ta musamman don su samar da ilimi ingantacce.Batun lafiya fa tunda lafiya uwar jikiBatun kiwon lafiya da duba mata masu ciki da shayarwa duk mun yi akqawari za mu ke bayar da magani kyauta. Fatanmu yin komai cikin farin ciki da ikhlasi don samar da al’umma lfiyayyiya ingantacciya.Me ne qalubalenki musamman wanda ki ka gani da idonki a zagayen da ki ke yi?Qalubalena shi ne yadda na ga mata babu abin yi sannan babu wadataccen ilimi sannan mata na kuka da yadda ba a cika musu alqawarurruka bayan zave. Wanda na yi musu alqawarin wannan matsala ta kau. Duk da ba a mugun sarki sai mugun Bafaxe to in sha Allah za mu sa ido sannan za mu xau mataki don tabbatar da wannan qalubalen da na gani ya kau.Wanne Kira za ki yi wa mata kan fita zave?Babban kira na shi ne don Allah mata ku fita ku je ku karvo katinan zavenku. Katinan nan da su , naku ne , birjik a ma’aikatar zave. Zaven nan nan mata ‘yancinmu ne. Mu mata an san mu da alqawari sannan an sanmu da tunani da kaifin basira don haka mu karvo kayanmu sannan ranar zave mu yi haquri mu jure mu kaxa quri’a kuma mu zavi APC daga qasa har sama nasara tamu ce da yardar Allah. Wannan kiran ba iya mata ba ne har da mazan. Wanda kuskure ne .duk inda ka ke son mutum in har ba ka da katin zave ba yadda za ka zave shi, Kuma dai ka tuna sai ka yi zaven ne burinka akansa zai cika, Ka tuna da quri’arka xaya za ka iya tabbatar da kujera.Kuma wannan kujerar in ka yi dacenta ko ba ka da rai wani naka zai amfana tunda an zavi mutum na gari. Don haka a je a karvi katin zave kafin a rufe, Sannan mata su daure sati biyu kafin zave kada su yi lalle saboda yatsunsu na’urar ta gan shi. Ana raxe –raxin kuna sayen katunan zave Wannan magana qarya ce kuma jita-jita. Ai an kama waxanda suke yi an kuma kai su ga hukuma. Ba ma yi ba mu tava sanyawa ba, Don haka ma maigirma Xan takarar Gwamna a jam’iyyar APC Dr Dikko Umar Raxxa ya ce “duk wanda aka gani da katunan zave ba bisa qa’ida ba a yi rahotonsa ga ‘yansanda kuma a kai shi kotu da aka tanada musamman don wannan laifin”. Ai mu Alhadlillah, mu muna da imanin cewa a wurin Allah muke nema sannan al’ummar jihar Katsina mutane ne wayayyu da suka san cancanta kuma zaven cancanta za su yi. Ba su da wanda ya fi Dr Dikko Umar Radda cancanta. Sannan muna son komai za mu yi mu yi shi da ikhlasi da tsoron Allah don haka in ka sayi kuri’a ai ka yi ha’inci, duk abu na ha’inci ba za ka samu Dr Dikko a ciki ba. Fatanki ga al’ummar jihar KatsinaBabban fatana shi ne a yi zave lafiya a kammala lafiya , sannan ranar zave a yi jam’iyyar APC daga sama har qasa. Mata da maza su fito su rama karamci da karamci.Na gode.