Zaharadeen Ishaq Abubakar
@ Katsina City News
Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina mai baiwa Gwamnatin Katsina shawara akan harkokin tsaro ya bayayyana cewa gwamnan katsina mai jiran gado Alhaji Dikko Umar Radda zai iya nasara akan harkokin tsaro.
Alhaji Ibrahim Katsina ya bayyana hakan ne,a hirar da yayi da jaridun Katsina City News inda ya bayyana irin tubalin nasarorin da gwamnatin Aminu Bello masari ta Gina na Nasara akan harkokin Tsaro.
Ibrahim katsina ya bayyana cewa A lokacin Masari ya iske matsalar tsaro a Katsina amma babu wani kokari ko aiki na maganin matsalar.
Wannan ya Sanya ta kara girmama, amma nan da nan ya dau matakai daban-daban ana daukar matakin ana samun darasi.
Wannan ya Sanya gwamnati ta bullo da hanyoyi daban daban Wanda har ya kai ta ga matsayi tayi Zarra ga sauran makwabtanta da suke da matsala Iri daya.
Ibrahim katsina yace, an wayar da kan mutane, an shigo da sarakuna, Malamai, attajirai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ta tsaro.
Ibrahim katsina ya kara da cewa, an yi doka, an horas da yan sakai da sai masu makamai,an samar da wata cibiyar tattara bayanai wadda ba a taba irin ta ba a duniya.
Ibrahim katsina yace gwamna mai jiran gado in Yazo dorawa zai yi an gama masa wasu muhimman ayyukan da zai Dora a saman su.
Ibrahim katsina yace tsaro magana ce ta karatun baya da nazarin gaba duk wani tubali an riga an Gina masa.
A hirar ya Kira, aiki tare da Masari a matsayin wani karatun ilmi mai zurfi mai zaman kanshi.
Yana amsar shawara kuma zai saurare ka zai kuma baka shawara.
Hirar da Ibrahim katsina wani bangarene na hirar da jaridun Katsina City News keyi da manyan jami an gwamnatin Aminu Bello Masari suna bayyana nasarorin da gwamnatin ta samu a shekaru takwas da hawan ta.
Zamu saki cikakkiyar hirar ta hausa ranar alhamis 4/5/2023. A dukkanin shafukan yanar gizo na jaridun Katsina City News da Jaridar Taskar labarai da The Links News.
Za a buga cikakkiyar hirar ta turanci a mujjalar katsina city news da sakin hirar ta turanci a ranar 10/5/2023.
Katsina city news
@ Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779