Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Dakta Mustapha Moh’d Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da ya amshi bakunci Kungiyar Ladon Alkhairi ta yakin neman zaben Sanata Yakubu Lado Danmarke a matsayin Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin Dakta Musa Gafai.
Mustapha Inuwa yace Dikko Raɗɗa yana daga cikin Mutanen da sukai adawa da tsayawa takarar Masaria 2015 yace shi ya sama da aka fita yaƙin neman zaɓen da akaje ko ina a jihar Katsina shi Dikko Charanci kadai yaje, shima a lokacin ranar zabe basu taɓuka abin kirki ba. Yace aje a duba record.
Yace gidan Muntari Lawal nanne tushen Adawa da Masari, inda ya bayyana Ibrahim Masari, Dikko Raɗɗa, Muntari Lawal ba Abu Ibrahim a matsayin masu adawa da tsayawa takarar Aminu Masarin.
Yace da aka zo tsaida Dantakarar Ciyaman na jam’iyya, sai suka turo Dikko, yayi takara dani saboda sunga manufarsu tazo daya, wai don kada inje ko ina tunda Masari nake yi. Inji shi. Yace alokacin an nemi ya janye, sai yace wai ya kashe Miliyan Biyar kuma sai ambiyashi, Aminu Masari shi ya bashi Miliyan Uku daga baya aka cika mashi.
Yace “Don haka Dikko Raɗɗa Saidai takarar sa yayi a Naira miliyan biyar ba jenyewa yayi ba.” Sana yace idan aka tashi rabon mukamai na jam’iyya ta ƙasa yazama dole sai am bar mashi na Katsina kuma haka akai, aka bashi National Social Welfare Secretary. Inji Inuwa
Mustapha ya bayyana cewa Dikko Radda ta sanar dashi wasu Abubuwa guda hudu da yasa baya son Aminu Bello Masari ya tsaya takarar Gwamna, yace kuma abinda ya fadi tabbas a cikin hankalins ya faɗa saboda da azumi ne, bayan shan ruwa muna tare wata rana a Abuja gidan Sanata Sadiq’Yar Aduwa, da ya gayyaceni shan ruwa, shi yasan anyi haka, amma ya musanta maganar sai in bayyana.
Akwai cikakken Video zamu sakar maku a shafukan mu na yanar gizo a www.katsinacitynews.com